Home » Aliartwork Ya Kaiwa Zakzaky Shugaban Yan Shi’a Ziyara

Aliartwork Ya Kaiwa Zakzaky Shugaban Yan Shi’a Ziyara

by bharatnamdev945@gmail.com
Aliartwork Ya Kaiwa Zakzaky Shugaban Yan Shi'a Ziyara

Jarumin Barkwancinnan Kuma Dan Wasan Hausa Mai Suna Aliyu Wanda Mutane Sukafi Saninsa Da Aliartwork Ya Kaiwa Shugaban Yan Shi’a A Nigeria Wato Sheikh Ibrahim Zakzaky Ziyara. Bayan Ziyarar Da Jarumin Ya Kai Wajen Ibrahim Zakzaky Ya Sha Zagi Kamar Yadda Zaku Kalla A Wannan Bidiyon.

Jarumin Mai Suna Aliartwork Wanda Akafi Saninsa Da Madagwal Ya Fara Shan Zagin Ne Bayan Ya Dora Hotonsa Da Shuagaban Yan Shi’a Zakzaky. Inda Jama’a Sukayi Caa Akansa Suna Ta Tsine Masa Albarka.

Idan Baku Manta Ba, A Baya-Bayannan Jarumin Suka Samu Matsala Da Sarkin Waka (Naziru M Ahmad) Daga Karshe Kuma Suka Sasanta. A Yanzu Haka Wasu Daga Cikin Mabiyan Nasa Suna Tunanin Cewa Bashida Kyakkyawar Halayene Yasa Yake Aikata Irin Wannan.

A Wata Bangaren Kuwa Masoyan Aliartwork Sunyi Ta Jifarsa Da Bakaken Kalamai, Kamar Wadanda Suka Ganshi Da Fir’auna Ko Shedan. Ashe Haka Aka Tsani Shi’a?

Aliartwork Ya Kaiwa Zakzaky Shugaban Yan Shi'a Ziyara

Leave a Comment