Home » Hanyoyi Goma Da Zaka Gane Mace Bata Sonka – Sirrin Masoya

Hanyoyi Goma Da Zaka Gane Mace Bata Sonka – Sirrin Masoya

Hanyoyi Guda Goma Da Zaka Gane Mace Bata Kaunarka

by bharatnamdev945@gmail.com
Hanyoyi Goma Da Zaka Gane Mace Bata Sonka

Kana soyayya da mace amma tana nuna maka kamar bata sonka ko kuma tana shigar maka da wasu halayya wadanda kaima baka san kansu ba. A wannan rubutu mun kawo muku manyan hanyoyi guda 10 inda zaka gane cewa bata sonka. Don haka ka daina wahalar da kanka ka tsaya ka fahimta ta hanyar karanta wadannan hanyoyi guda goma da muka kawo muku yau.

Yadda Zaka Gane Mace Bata Sonka

Yawan Roko

Idan mace bata sonka to zata ringa yawan rokonka abun hannunka. Ba sai ka bata ba zakaga kawai tana tambayarka. Kuma abun takaicin shine duk tambayar da zatayi maka babu ruwanta da yin la’akari cewa kana dashi ko baka dashi. Domin duk abinda ya fado mata a rai kuma taji tana bukata to kawai zata tambaya ne.

Bazata Ringa Kiranka Ba

Idan mace bata sonka to kaida ganin kiranta sai bayan ranka. Ina nufin indai kiranka ne zatayi a waya to sai dai kawai ka mutu. Domin ba zata taba nemanka a waya ba. Idan ma tana da wata bukata da kai saidai kawai tayi maka flashing. Kullum kawai ita akan flashin zata kare. Kuma koda ace zaka tura mata kati zakaji tana cewa ya kare ko babu.

Fara’a Da Murmushi

Idan tana sonka ba don kudinka ba to kawai duk wani murmushi da zatayi maka na shiri ne. Zatayi maka murmushi ne da saukar da kai a lokacin da take da bukatar wani abu a wajenka kawai.

Maganar Aure

Maganar aure ba zai taba shiga tsakaninku da ita ba, Duk wani abu da zai janyo maganar aure to zatayi kokari ta matsar dashi gefe ne. Domin ita bukatar ta ba aure bane. Bukatarta kawai shine ta samu ta tsatseka wasu yan kudade, shikenan.

Karban Waya

Idan bata sonka tsakaninta da Allah to bazata taba yarda ka karbi wayarta ba har kace zaka duba ba. A kullum ita zatayi kokari taga ta nesantaka da wayarta. Ganin cewa waya shine yanzu yake dauke da duk wani abu na mutum. Saboda haka zatayi iya bakin kokarinta wajen ganin ta rabaka da wayarta.

Mu’amala

Mu’amalarka da macen da bata sonka yana da saukin ganewa. Domin ita akoda yaushe babu ruwanta da meye alakar ku. Bazata so ku ringa kasancewa a tare ba harma jama’a suce akwai alaka tsakaninku.

Ziyara

Duk macen da bata sonka maganar ziyara zata watsar dashi a gefe. Domin shi ziyara yana kara dankon soyayya. Musamman ma ziyara ga yan uwa da sauran dangi.

Nuna Soyayya Ga Yan Uwa

Duk macen da bata kaunarka babu ruwanta da danginka ko yan uwanka. Bazata taba tambayarka yaya mamanka take ba, babanka, ko kennanka.

Shawari

Idan mace bata sonka to bazata taba tambayarka shawari ko wani abu dangane da rayuwarka ba. Ita dai burinta kawai ka bata. Ba iya wannan ba, idan mace bata sonka to bazata ringa nemanka da shawara ko neman mafita akan wani abu da ya shigeta mata duhu na rayuwa ba. Ita kullum tunaninta ya za’ayi ka rabu da ita.

Kalamai

Daga kalamanta kana iya gane bata sonka. Musamman ma idan tana shigar maka da wasu kalaman da basu shafeka ba, ko kuma baka gane kan kalaman. zata ringa shigar maka da bakaken maganganu a hankali ta yadda bazaka lura ba. Idan tayi magana ka nuna maka gane ba, sai tce a mantar da maganar, amma babu zancen kalaman soyayya.

Yadda Zaka Gane Mace Bata Sonka

Hanyoyi Goma Da Zaka Gane Mace Bata Sonka

Wadannan Sune hanyoyi guda goma manya da zaka gano macen da bata sonka cikin sauki. Zaka iya fahimtar hakan a hankali idan ka lura. Haka zalika kuma zai iya yiwuwa ta ringa nuna maka halayen a boye.

Karanta:

Yadda Asirin Mazan Kano Ya Tonu! Budurwa Ta Bayyana Yadda Mazajen Kano Suke

Leave a Comment